Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Abubakar Lawan ya fara aiki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya raba wa manema labarai.
Sauyin nasa ya biyo bayan ritayar CP Isma’ili Dikko ne bayan ya shafe shekaru talatin da biyar yana aiki.
DAILY POST ta ruwaito cewa, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Baba ya bayar da umarnin tura sabbin kwamishinonin ‘yan sanda biyu na jihohin Kano da Zamfara.
CP Abubakar shi ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano na 43, an haife shi ne a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 1965 a karamar hukumar Daura ta jihar Katsina. Ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria inda ya sami digiri na farko a fannin zamantakewa.
Ya rike mukamai da dama kafin a bashi mukamin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, ya kasance kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Enugu.
Ya kuma halarci kwasa-kwasan ƙwararru da na jagoranci da tarukan karawa juna sani da bita a ciki da wajen ƙasar nan.


