Guda daga cikin masu yi wa ministan birnin tarayya, Nyesom Wike biyayya, Isaac Kamalu, ya yi murabus daga mukamin kwamishinan kudi na jihar River, bayan da gwamna Simi Fubara ya mayar da shi ma’aikatar samar da ayyukan yi da karfafa tattalin arziki.
Kamalu wanda ya taba rike mukamin kwamishinan kasafi da tattalin arziki a karkashin tsohon Nyesom Wike, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wata wasika da ya aikewa gwamna Fubura da sakataren gwamnati Tammy Danagogo.
Ya zargi Fubara da yin karya game da kudaden shigar da ake samu a jihar Ribas.
Tun da farko dai, Zacchaeus Adangor, kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, ya yi murabus, saboda irin wannan batu.
Wannan lamari dai na zuwa ne watanni bayan da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Fubara da Wike a wani rikici da ya barke tsakanin bangarorin biyu.
Ko a baya dai a rikicin Fubara da Wike, Kamalu ya yi murabus daga mukamin kwamishina, amma aka mayar da shi, bisa yarjejeniyar zaman lafiya.