Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Zamfara, ZASIEC, Hashimu Shehu Gazura, ya rasu a wani hatsari da ya yi.
Gazura wanda ya taba wakiltar mazabar Gummi ta 2 a majlisar jihar, ya rasu ne sakamakon hatsarin da ya yi a kan titin Yawuri Kamar yadda shugaban hukumar majalisar jihar, Mansur Bungudu ya sanar, ya ce, za a yi jana’izarsa a ranar Asabar a fadar sarkin Gummi.
Hatsarin ya auku ne kan titin Yawuri da ke jihar Kebbi a ranar Juma’a kamar yadda TheCable ta rawaito. Mansur Bungudu, shugaban hukumar majalisar jihar Zamfara, ya sanar da rasuwar Gazura a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar.