Rashid Bawa, babban kwamishinan Ghana a Najeriya ya rasu.
Ya rasu ne a Abuja, babban birnin Najeriya.
Bawa, wanda shugaba Nana Akufo-Addo ya nada kan wannan mukami a shekarar 2017, an ruwaito ya rasu ne a ranar Alhamis.
Memba na Sabuwar Jam’iyyar Patriotic Party (NPP) kuma fitaccen jami’in diflomasiyya, Bawa ya taba zama jakadan Ghana a Saudiyya daga 2005 zuwa 2008.
Ya kuma wakilci mazabar Akan a majalisar dokokin Ghana a matsayin dan takara mai cin gashin kansa daga 2001 zuwa Janairu 2005.
Mutuwar Bawa na zuwa ne jim kadan bayan rasuwar John Kumah, mataimakin ministan kudi na Ghana kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Ejisu.
Shugaba Akufo-Addo ya yaba wa Kumah bisa jajircewarsa na yi wa kasa hidima da kuma jajircewarsa na inganta rayuwar ‘yan Ghana.
Shugaban ya ce, “Jajircewar sa na hidima, da jajircewarsa na ci gaban al’ummarmu, da kuma tsananin kishinsa na daukaka rayuwar al’ummar Ejisu da Ghana sun bayyana ga duk wanda ke da damar saninsa.”