Tsohon kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi na jihar Kano, Nura Dankadai, ya fice daga jamâiyyar All Progressives Congress (APC).
Ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya aike wa shugaban gundumar Tsohon Gari da ke karamar hukumar Tudun Wada.
A watan Afrilu ne Dankadai da sauran kwamishinoni suka yi murabus daga mukamansu, domin tsayawa takara a mukamai daban-daban kamar yadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba su umarni.
Ya nuna shaâawarsa tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa.
Duk da cewa bai bayyana alkiblar sa ta gaba a hukumance ba, amma ana ta rade-radin cewa, zai koma jamâiyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Rabiâu Kwankwaso.