Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi ya gurfana a gaban kwamitin bincike kan takaddamar belin wani da ake zargi da sayar da miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu a daren jiya.
.
A cikin wasikar murabus din da ya aikewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin murabus ne saboda fifikon maslahar al’umma da kuma la’akari da yanayin da al’amarin yake ciki.
.
Wasikar murabus din tana kunshe ne cikin sassa ‎“A matsayina na memba a gwamnatin da ta ci gaba da fafutukar yaki da tallace-tallace da shaye-shayen miyagun kwayoyi, ya zama wajibi in dauki wannan matakin — mai raɗaɗi kamar yadda ya kamata.
.
“Yayin da nake ci gaba da kasancewa da fuskantar tuhuma, ba zan iya yin watsi da nauyin ra’ayin jama’a da kuma bukatar kare kimar da muka gina tare,” in ji shi.
.
Alhaji Namadi ya bayyana matukar godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya samu na yi wa jihar hidima, tare da jaddada sadaukarwar sa ga tsarin shugabanci nagari da kuma shugabanci na gari.
.
“Dole ne a matsayina na dan kasa nagari, in yi kokarin karewa, kiyayewa, da kuma tabbatar da amana da hangen nesa da muka yi aiki tukuru wajen ganin mun kafa wannan jiha tamu.
.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din tare da yi wa tsohon kwamishinan fatan samun nasara a ayyukan sa na gaba.
Ya kuma nanata matsayar gwamnatinsa na rashin gaskiya a kan adalci, da’a, da yaki da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi da munanan dabi’u da suka shafi matasa da sauran al’umma.
Gwamnan ya kuma kara jaddada bukatar dukkan masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amura masu muhimmanci tare da samun izini daga babbar hukuma a duk lokacin da za su tsunduma kansu a kan batutuwan da suka shafi al’umma.
.