fidelitybank

Kwamishina mai ci a PDP ya sauya sheƙa zuwa APC a Sokoto

Date:

A karshen mako ne kungiyar APC reshen jihar Sokoto, ta karbi bakuncin kwamishinan ayyuka da harkokin tsaro na jihar Kanar Garba Moyi Isa mai ritaya.

Moyi, wanda dan jam’iyyar PDP ne, ya ga rashin amana da mayar da hankali a matsayin dalilansa na sauya sheka zuwa APC.

Naija News ta fahimci cewa, Moyi ya samu karbuwa a cikin jam’iyya mai mulki ta kasa ne daga hannun shugaban jihar, Sen. Aliyu Magatakarda Wamakko.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai ga Sanata Wamakko, Bashar Abubakar ya fitar.

Da yake yi wa Moyi tarba mai kyau a gidansa, Wamakko ya bukaci Moyi da ya tabbatar da yin aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, don samun nasara a yankin Sanatan Sokoto ta Gabas da ma jihar baki daya a zaben 2023 mai zuwa.

Naija News Hausa ta fahimci cewa, Moyi ya samu rakiyar mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Gawon Nama Sokoto, gidan Sanata Wamakko. Idris Muhammad Gobir; Dan takarar Sanatan APC, Hon. Ibrahim Lamido Isa da Dan Takarar Majalisar Wakilai ta APC, Hon. Abdulkadir Jelani Danbuga; da kuma shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Yawale Sarkin Baki.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp