Haduran mota da aka samu daban-daban a karshen mako, sun yi sanadiyyar mutuwar motum 30 tare da raunata wasu da kuma asarar dukiya.
Hukumomin sun danganta haduran da saba ka’idojin hanya da gudun da ya wuce kima da kuma tafiye-tafiyen dare.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, daga cikin haduran, wasu da suka auku a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi, sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 18 a gadar Isara da ke jihar Ogun, kan tagwayen hanyar Lagos zuwa Badun.
Sannan wasu mutum 10 sun rasu a kan titin Potiskum zuwa Gombe a Jihar Yobe, yayin da wasu mutum biyu suka rasu a wani hadarin motar a kan titin Lokoja zuwa Obajana zuwa Kabba.
A hadari na hudu, wanda shi kuwa ya rutsa ne da kwambar motocin Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, a Abuja, rahotanni sun ce, motoci hudu wasu tireloli biyu suka murkushe, yayin da wata motar jami’na tsaro a kwambar ta yi karo da wata motar kirar Golf, sai dai ba wanda ya rasa ransa, a hadarin.