Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin fili yana sharɓar kuka bayan da Santos tasha kashi da ci 6-0 a gida a hannun Vasco da Gama.
Karon farko da Neymar aka ci su ƙwallaye da yawa a tarihi yana cikin fili, kuma a karon farko da zura ƙwallaye da yawa a ragar Santos kuma a gida a babbar gasar tamaula ta Brazil.
Tuni ka kori kociya Cleber Xavier, bayan tashi daga wasan na ranar Lahadi, sai dai Santos mai rike da kofin gasar Brazil karo takwas tana da maki biyu tsakaninta da ƴan karshen teburi.
Xavier, mai shekara 61, ya karɓi aikin a watan Afirilu, bayan da ya yi mataki a ƙungiyoyin dake buga gasar lik ta Brazil da kuma a tawagar ƙwallon kafar kasar.
Santos, wadda ta koma buga babbar gasar tamaula ta Brazil a watan Nuwamba, bayan zama a Serie B ta yi nasara biyar daga karawa 15.
Ranar 24 ga watan Agusta, Santos za ta buga wasan gaba da Bahia.