fidelitybank

Kwalejin Kimiya da Fasaha a Kano ta kori ɗalibai

Date:

Kwalejin Kimiyya da Fasahar lafiya ta Aminu Dabo dake Kano ta kori dalibai 12, bisa samun su da laifin satar amsa a lokacin da suke rubuta jarabawa.

Wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na kwaleji, Abdullahi Usman ya fitar a ranar Talata, ta ce an kama wasu dalibai 13 (‘yan aji 2) bisa laifuka daban-daban da suka shafi rashin da’a a yayin gudanar da jarrabawa a makarantar.

Sanarwar ta ce an kama  daliban suna tafka magudin jarrabawa da rashin da’a wanda ya saba wa ka’idojin Kwalejin a lokacin jarrabawar zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Sanarwar ta ce, ”Hukumar Kwalejin ta dauki mataki  kan daliban ne, Saboda abin da  su ka yi ya saba da dokar makarantar, inda a ka yi amfani da shawarwarin da kwamitin ladabtarwa ya bayar.

Rahotanni sun nuna cewa, daliban da abin ya shafa an kama su da hannu dumu-dumu cikin rashin da’a da kuma wasu abubuwa da suka saba wa tsarin kwalejin a lokacin jarrabawar.

Hukumar gudanarwar, ta umurci sauran daliban da aka wanke da su koma kwalejin a ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, 2022, domin ci gaba da jarrabawa tare da gargaɗin sauran ɗaliban.

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp