fidelitybank

Kwale-Kwale ya kife da mutane 40 a Zamfara

Date:

Wani mummunar hatsarin kwale-kwale yayi sanadin nutsewar fiye da mutum 40 a garin Gummi na jihar Zamfara.

Shaidu sun tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar, a mashayar ‘yan daga da ke gulbin Gummi.

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Abubakar Umar ya ce har ya zuwa yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutanen da suka nutse.

”Kawo yanzu sarkin ruwan yankin da sauran masu iyo na ci gaba da aikin ceto, don lalubo mutanen da kwale-kwalen ya kife da su, kuma kawo yanzu ko mutum guda ba a kai ga cetowa ba”, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ƙara da cewa galibi waɗanda ke cikin jirgin manoma ne da ke ƙoƙarin tsallaka kogin domin zuwa gonakinsu.

Kwamishinan yaɗa labarai da bunƙasa al’adu na jihar, Mannir Haidara Kaura ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sai dai ya ce kawo yanzu a hukumance ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba.

Ya kuma ƙara da cewa an ceto wasu daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su, kuma ana ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo mutanen da suka nutse cikin ruwan

Hatsarin na zuwa ne makonni bayan mummunar ambaliya ruwa da auka wa garin na Gummi, inda ta haddasa asarar dukiya mai ɗimbin yawa.

Batun kifewar kwale-kwale dai ba sabon abu ba ne a Najeriya, inda a lokuta da dama hatsarin ke zuwa da muni sakamakon irin ƙazamin lokdin da ake yi wa jiragen ruwan.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp