fidelitybank

Kwale-Kwale ya kafe tare da mutuwar mutane 20 a Binuwai

Date:

Akalla mutane 20 ne aka ruwaito sun mutu bayan wani jirgin ruwa ya kife a kogin Benue a ranar Asabar.

Rahotanni na cewa kwale-kwalen nasu ya kife ne a lokacin da suke tsallakawa daga Ocholonya a karamar hukumar Agatu zuwa Odenyi a karamar hukumar Nasarawa Toto ta jihar Nasarawa bayan gudanar da ayyukansu a kasuwar Ocholonya.

Wani shaidan gani da ido, Fada Awatsu ya ce, “kwale-kwalen katako na cike da kaya da fasinjoji daga kasuwar Ocholonya.

“An yi lodi fiye da kima kuma jim kadan da tashinsa sai fasinjojin da ke cikin jirgin suka yi hayaniya kuma daga karshe ya fadi ya gangara cikin ruwa.”

Sun fito ne daga Agatu, Agbashi, Ajima, Okpata, Rukubi, Ondoli, Odadu a karamar hukumar Doma.

Majiyoyi sun ce wadanda abin ya shafa mata ne da kananan yara da ke dawowa gida daga kasuwa.

Ya zuwa yanzu dai an gano gawarwaki 19 daga hatsarin, yayin da ake ci gaba da aikin ceton wasu.

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Agatu, Hon.Melvin Ejeh ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “wadanda aka kashen suna dawowa ne daga kasuwar Ocholonya zuwa kauyensu da ke kusa da jihar Nasarawa.

“Bishiyoyi a cikin kogin sun hana ganin ma’aikacin jirgin kuma lokacin da kwalekwalen ya bugi bishiyoyi, ya fado ya kife.”

Hon Ejeh ya ce an gano gawarwaki sama da 20 kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Ya ce zai tura jami’an majalisar domin yi wa iyalan mamacin ta’aziyya.

nigeria news today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp