Tun bayan da kotun ƙoli ta yanke hukunci game da ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai-tsaye daga asussun gwamnatin tarayya, ake ta sa ran ganin alfanun da hakan zai haifar, musamman ga mutanen karkara da suka fi zama kusa da ƙananan hukumomin.
Sai dai ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin ta ƙasa, ALGON, ta bayyana wa BBC cewa, kuɗaɗen da za a ware masu ba za su isa ko da biyan albashi mafi ƙaranci ba.
A kasafin kuɗin wannan shekarar dai an ware wa ƙananan hukumomin kimanin Naira triliyan biyu.