Gwamnatin ƙasar Kuwait ta jaddada aniyarta ta tallafa wa yara 200,000 da ba su zuwa makaranta a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Jakadan Kuwait a Najeriya, Salim Almuzayen ne ya sanar da yunƙurin yayin taron Ranar Ƙasa ta Kuwait karo na 64 da aka gudanar a Abuja, kamar yadda kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
Almuzayen ya yi bayanin cewa shirin zai taimaka wajen samar da ingantaccen ilimin firamare ga yara musamman masu larura ta musamman, da mata, da ma manya a Kaduna.
“Hakan na nuna ƙwarin daɗewar alaƙa [tsakanin Najeriya da Kuwait] da kuma irin yadda za mu ci gaba da aikin haɗin gwiwa tun daga shekarun 1960 – lokaci da aka gina makarantar Al-Sabah a Kaduna,” a cewar jakadan.