Rasha ta ce akwai hannun ƙungiyar tsaro ta Nato da kuma ƙasashen yamma a kutsen da Ukraine ke yi cikin yankin Kursk na Rasha.
Cikin wata hira da wata jarida ta Izvestia ta yi da wani jami’in gwamnatin Rasha Nikolao Patrushev, ya ce suna ganin irin abubuwan da sojojin Ukraine ke yi a yankin Kursk, akwai hannun ƙasashen yamma da kuma ƙungiyar tsaro ta Nato a ciki. In ji BBC.
Ya ce,” Sanarwar da Amurka ta fitar cewa babu hannunta a irin kutsen da Ukraine ke yi a yankin Kursk, ba gaskiya bane, saboda idan har babu hannunsu babu yadda za a yi Ukraine ta rinka abin da ta ke a yanzu a yankunan Rasha.”
A farkon makonnan ne Amurka ta fitar da sanarwar cewa bata da masaniya a kan irin abubuwan da Ukraine ke yi kuma babu hannunta ko koɗan.”
Ukraine dai ta ce sojojinta na ci gaba da nausawa cikin yankunan Rasha har ma ta kafa wani ofis na sojojinta a Rasha.
Ta ce, ‘Za mu ci gaba da kafa ofisoshi ma a duk yankin da muka ƙwace’
A baya bayannan dai sojojin Ukraine suka kai wani harin bazata zuwa lardin Kursk na Rasha, da ke maƙwabtaka da ita. Sai dai an kasa samun sahihan bayanai kan wannan hari da aka kai kawo yanzu.
Tun da farko, an yi tsammanin cewa wasu ƙungiyoyi masu zagon ƙasa ga Rasha ne waɗanda ke adawa da gwamnatin shugaba Vladimir Putin suka kai harin.
Ukraine ta yi amfani da rashin isassun jami’an tsaro a kan iyaka wajen kutsawa zuwa cikin Rasha, a yayin da Rasha ta karkata aƙalar sojojinta zuwa wurare daban-daban da ake ci gaba da gwabza fada