Hukumar yi wa Malaman Makaranta Rijista ta Najeriya (TRCN) ta bayyana cewa kimanin malaman makaranta dubu uku da dari tara da sittin da uku ne suka faɗi jarrabawar da ke nuna ƙwarewa da suka zana a watan Nuwamban wannan shekara ta 2023.
Hukumar ta ce malamai dubu goma sha biyar da dari bakwai da hamsin da uku ne suka zauna jarabawar, daga ciki dubu goma da dari shida da talatin da shida suka samu nasara, yayin da dubu uku da dari tara da sittin da uku suka fadi.
Wannan lamari ya sa masana a ɓangaren ilmi a Najeriya yin tsokaci game da batun.
Masana irin su Dakta Aliyu Umar Tilde, tsohon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, ya ce jarabawa ce mai kyau saboda “da yawa daga cikin malamai, ana samu suma kansu suna buƙatar karatu.”
Ya ba da misali da jihar Kaduna inda a kwanakin baya, aka yi wa malamai jarabawa kuma da yawan su suka faɗi.
“Sanin cewa akwai rauni wajen horar da malaman shi ne ya sa dole a samar da jarabawa kafin a ba da lasisi”, kamar yadda masanin ya ce.
Ya ce a baya, ba a irin wannan jarabawa ta tantance ƙwarewar malami saboda karatu a lokacin yana da ƙarfi a makarantu “amma daga baya da makarantu suka yi yawa, har da na jeka na yi ka, akwai kuma yaudara da shaidar karatu ta bogi, wannan shi ne ya tilasta cewa ya kamata a jarraba ka kafin a tabbatar.” in ji Dakta Tilde.
Ya bayyana cewa akwai buƙatar a yi gyara sosai a ɓangaren ilimi na Najeriya idan ana son tsarin karatu ya koma irin na shekarun baya, lalacewar gwamnati shi ne ya haifar da lalacewar ilimin, a cewarsa.
Masanin ya ce sai an samu gyara ta ɓangaren gwamnati da su kansu malaman sannan al’amura za su daidaita a tsarin ilimin ƙasar.