fidelitybank

Kurunkus: Ganduje ya nuna wanda zai gaji kujerarsa a 2023

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya zaɓi mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a babban zaɓe na 2023.

Wasu majiyoyi a fadar Gwamnatin Kano, sun shaida wa BBC Hausa cewa, an cimma matsayar ce yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulkin Kano da aka gudanar a yau Asabar.

Sai dai wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta faɗa wa BBC Hausa cewa, har yanzu ba a kai ga daddale wannan zaɓi ba a hukumance.

Kazalika, an ruwaito cewa taron ya amince Kwamashinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu Murtala Sule Garo ya zama mataimakin Gawuna a takarar ta su.

Ana kallon matakin a matsayin wani sauyi daga goyon bayan da Murtala Garo ke samu na wasu jiga-jigan gwamnatin, ciki har da matar gwamna Hajiya Hafsat Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin Ganduje.

Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar wa ɓangaren Ganduje shugabancin APC a Kano, sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaɓukan shugabanci a watan Oktoba tsakaninsa da ɓangaren tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau.

nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp