‘Ya’yan kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun yi wa ginin majalisun dokokin na tarayya tsinke da tsakar ranar Talata, inda suka garkame kofar shiga ginin, a wani yunkuri na tursasa yajin aikin da suka kira a fadin Najeriya.
‘Yan kwadagon sun tafi yajin aikin ne daga daren Talata sanadin wata takaddama tsakaninsu da gwamnatin Najeriya.
Rahotanni sun ce tun daga misalin karfe 11:45 ne, masu yajin aikin suka hana ma’aikatan majalisa da baki masu zuwa, shiga ko fita daga harabar ginin.
Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ‘yan majalisar da suka riga suka shiga zaurukan majalisar biyu sun ci gaba da gudanar da ayyukansu, kamar yadda suka saba.


