Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC ta TUC a Najeriya, sun fara gudanar da zanga-zanga ta ƙasa baki daya don nuna rashin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
Shugabanni da mambobin ƙungiyar da dama sun taru a fitaccen dandalin ‘Unity Fountain’ da ke tsakiyar Abuja babban birnin ƙasar, riƙe da tutoci da allunan da ke ɗauke da saƙonni daban-daban.
Haka kuma rahotonni daga sassan ƙasar daban-daban sun nuna cewa tuni ƙungiyoyin suka fara gudanar da zanga-zangar a fadin jihohin ƙasar.
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya wakilinmu ya ce ɗaruruwan mambobin ƙungiyar ne ciki har da mata suka fito domin gudanar da zanga-zangar
A ranar Litinin ne shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya yi wani jawabi ga ‘yan ƙasar, inda a ciki ya jajanta wa `yan al’ummar ƙasar dangane da halin matsi da matakin janye tallafin ya jefa su ciki, amma ya ce babu wani zabin da ya fi janye tallafin.
Sannan shugaban ya sanar da wadansu matakai da gwamnati ta ɗauka don rage raɗadin janye tallafin.
Sai dai kungiyar kwadagon ta ce babu wani tasiri da za su yi wajen rage wa al`umma ukuba.