Kungiyoyin masu fafutikar kare haƙƙin mata a Ivory Coast na adawa da wani kuɗirin dokar da ya halasta wa maza auren mace fiye da daya a ƙasar.
Suna masu cewa matakin wani koma baya ne a yaƙin da suke na neman daidaito.
A 1964 ne dai aka hana auren mace fiye da ɗaya a Ivory Coast.
Auren mace fiye da ɗaya ba sabon abu ba ne a ƙasashen yammacin Afirka saɓanin wasu ƙasashe na duniya.
Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ɗauki auren mace fiye ɗaya a matsayin nuna wariya ga mace tare da kiran a kawar da tsarin. In ji