fidelitybank

Kungiyoyin Addinai sun buƙaci a janye zanga-zanga

Date:

Majalisar jagororin addinai ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta ƙasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar III, da shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN). Archbishop Daniel Okoh ya yi kira da a gaggauta kawo ƙarshen zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da ke gudana a faɗin Najeriya

Sun yi wannan kiran ne a yau Juma’a cikin wata sanarwa da suka sanyawa hannu tare da babban sakataren majalisar NIREC, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua.

“Majalisar NIREC ta lura da abubuwan da ke faruwa a ƙasar a halin yanzu. Zanga-zangar wanda aka faro cikin lumana a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 ta ɗauki wani salo na tashin hankali daga baya.

Sanarwar ta ƙara da cewa “A cikin ƴan sa’o’i kaɗan an yi asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon wannan mummunan yanayi.”

Majalisar ta amince da cewa ana fuskantar wahalhalu da dama a ƙasar amma ta ce tashin hankali ba shi ne mafita ba, inda ta ƙara da cewa hakan zai ƙara dagula halin da al’ummar ƙasar ke ciki.

“NIREC tana kira ga ƴan Najeriya da su janye wannan zanga-zangar su baiwa gwamnati damar wanke kanta.” In ji sanarwar

NIREC ta buƙaci gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakai domin biyan buƙatun ƴan ƙasar.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp