fidelitybank

Kungiyar TNM za ta samar da mafita a 2023 – Kawu Sumaila

Date:

Tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara kan al’amuran Majalisar Wakilai, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya ce, sabuwar kungiyar siyasar nan ta TNM za ta sama wa ‘yan Najeriya mafita a 2023.

Kawu, wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya na cewa siyasar Najeriya na bukatar kungiya irin TNM.

Ya ce, “Ina goyon bayan wannan tafiya saboda za ta farfado da dimokuradiyya ta kuma samar da shugabanci na gari, ci gaba da sauran manyan nasarori”, inji shi.

Kazalika, Kawu ya ce, zai goyi bayan duk wata tafiya da za ta karfafa dimokuradiyya kafin babban zaben 2023, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin da ke tsakaninsa da wasu ba.

Tsohon dan majalisar ya kara da cewa wadanda suka kirkiri tafiyar ta TNM mutane ne da ke da tarihi da kwarewa a fagen siyasa.

“Wadanda suka kirkiri wannan tafiya ta TNM da tsarinta sun shirya sosai. Ina murna saboda yawancinsu suna da gogewa a harkar siyasa,” inji tsohon dan majalisar.

Aminiya ta rawaito cewa, masu sharhi a kan al’amuran siyasa dai na ganin zai yi wuya a samar da wata kungiyar siyasa a wannan lokacin har ta yi tasiri a zabukan 2023.

Ko gabanin zabukan 2019 ma wasu jigajigan ”yan siyasa sun yi yunkurin samar da wata tafiya da juya akalar siyasar Najeriya, amma daga karshe ba ta sake zane ba.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp