Ƙungiyar Tarayyar Turai ga gargaɗi jiragen samanta su kauce wa bi ta sararin samaniyar ƙasashen Isra’ila da Lebanon zuwa wata mai zuwa.
Hukumar kula da kariyar sufurin jiragen sama na ƙungiyar Tarayyar Turan (EASA), ne ya fitar da gargaɗin ga duka jiragen saman ƙasashen mambobin ƙungiyar, har sai ”nan da 31 ga watan Octoba”.
“EASA za ta ci gaba da lura da yanayin, domin duba yiwuwar ƙara ko rage wa’adin, la’akari da ƙari ko ragin barazanar hatsari”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.


