Sakatare janar na ƙungiyar Commonwealth ta nuna matuƙar damuwarta kan halin da Gabon ke ciki bayan juyin-mulkin sojoji, tana mai cewa ƙungiyar na bibbiyar abubuwan da ke faru.
Patricia Scotland ta ce akwai damuwa mai tsanani kan yada abubuwa ke kasancewa: “Ya zama dole ƙasashen wannan ƙungiya su mutunta doka da dimokuraɗiyya a kowanne lokaci.”
Gabon ta shiga wannan ƙungiyar ta reinon Ingila a Yunin 2022 domin rage karfin dogaro da Faransa – ƙasar da ta mulkesu kafin ‘yanci.


