Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’I ta kasa, SSANU, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta biyan ma’aikatanta albashin watanni hudu da ta rike.
Shugaban SSANU na Jami’ar Tarayya ta Lokoja, Adedeji Suarau, ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis a Lokoja cewa, har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta biya ma’aikatanta albashin watan Mayu da Yuni tare da Yuli da kuma Agusta 2022.
Suarau, ya bayyana cewa, a kwanakin baya gwamnati ta biya malaman jami’o’in albashin da aka hana su, ya kara da cewa zai zama kawai gwamnati ta biya mambobin SSANU.
Gwamnatin tarayya ta hana mambobin SSANU albashin watanni hudu saboda shiga yajin aiki a shekarar 2022.
A cewar Duk kokarin da ake na ganin an biya ma’aikata albashi ya ci tura a lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na lokacin.