Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK), ta gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Talata, inda ta bukaci gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da aka sake tattaunawa tare da biyan albashin da aka hana.
Mataimakin Shugaban ASUU-BUK, Kwamared Yusuf Madugu, ya shaida wa manema labarai a Kano cewa, matakin ya zama dole sakamakon gazawar gwamnati wajen magance bukatun kungiyar.
Ya tuna cewa kungiyar ta shiga yarjejeniya tun a shekarar 2009, wacce aka sake tattaunawa da kwamitoci daban-daban na gwamnati ƙarƙashin jagorancin Farfesa Munzali Jibrin, Farfesa Nimi Briggs, sannan daga baya ƙarƙashin Malam Yayale Ahmed.
“An kammala tattaunawar a watan Disamba 2024, amma har yanzu gwamnati ba ta ɗauki mataki ba,” inji Madugu.
“Wannan shi ne matakin farko daga cikin matakai da dama da za mu ɗauka don jawo hankalin gwamnati. Dole gwamnati ta biya bukatunmu.”
Ya ce daga cikin albashin watanni bakwai da rabi da aka hana malamai lokacin yajin aiki, an biya watanni hudu kacal, sauran watanni uku da rabi suna nan babu biyan.
Batun Inga