Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya za ta yi wani taro na manyan shugabanninta, domin daukar matakin da ya kamata bayan da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cire tallafin mai, abin da ya sa farashin ya tashi kusan ninki uku.
Sakataren kungiyar Nasir Kabir ya sheda wa BBC cewa shugabannnin za su yi wannan ganawa ne ta hanyar intanet ta Zoom.
Tun bayan furucin da Shugaba Tinubun ya yi ne kasar wadda ta fi yawan jama’a da kuma kasancewarta gaba-gaba a arzikin mai ta fada wani yanayi na tashin farashin man da kuma dogayen layin ababan hawa a gidan sayar da mai.
Yanzu dai layikan kusan sun ragu kasancewar yawancin gidajen mai a manyan biranen kasar suna amfani da farashin da ya kama daga naira 500 zuwa 600.
Kamfanin man fetur na Najeriyar, NNPC ya tabbatar da cewa ya ƙara kuɗin litar mai a ƙasar.
A wata sanarwa da ta kamfanin ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce ya yi karin farashin domin ya yi daidai halin da ake ciki.
Kuma ya roƙi afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa.
Kafin yanzu dai ana sayar da man a farashin da ya kama daga naira 180 zuwa naira 220 kan kowa ce lita, a sassan kasar daban-daban.
Tun da aka shiga yanayin kungiyar kwadagon ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan batun janye tallafin man.
Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda cire tallafin zai jefa al’umma a cikin wahala.
Sayar da man a farashi mai yawa ana ganin zai kara irin wahalhalun da jama’a ke sha a kasar wadda dama tuni take fama da matsaloli na bunkasa da kuma tsadar rayuwa wadda ba ta taba gani ba a kusan shekara ashirin baya.


