Ɗaruruwan masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Abuja, sun nufi majalisar dokokin ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, kwamared Joe Ajeoro ne yake jagorantar zanga-zangar.
Wakilin BBC Hausa da ke inda ake zanga-zangar ya ruwaito cewa jami’an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da na Civil Defense na ƙoƙarin hana su shiga harabar majalisar.
Sai dai a cewar wakilin BBC duk da turjiyar da jami’an tsaro suka nuna don hana ƴan ƙwadagon shiga harabar majalisar, hakan bai hana su ture shingen da aka saka ba inda suka shiga da ƙarfi sakamakon yawan da suke da shi.
Masu zanga-zangar dai sun toshe manyan hanyoyin da suka haɗa tsakiyar birnin tarayya Abuja.
Sun fara taruwa ne a hedikwatar NLC a Abuja inda a yanzu suka nufi majalisar dokokin ƙasar.