A yunkurin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi ya sake fuskantar tasgaro, yayin da ƙungiyar kwadago ta kara fice daga taron kwamitin ganawa da na gwamnatin tarraya a yau dinnan.
Rahotanni na cewa, kungiyar kwadagon ta fusata ne a lokacin da Gwamnatin Tarayya ta mika mata tayin Naira 57,000 zuwa 60,000.
Sai dai kungiyar kwadago ta dage a kan sai gwamnatin tarayya ta bayar da albashi mafi karanci na Naira dubu 494.
Sai dai taron ganawar nay au, bai samu halartar wasu gwamnoni da ke cikin kwamitin bangarori uku ba da fadar shugaban kasa ta kafa kwanan nan.