fidelitybank

Kungiyar kwadago na zanga-zanga a kan kara kudin wutar lantarki

Date:

A yau Litinin ne ƙungiyar ƙwadago NLC da takwararta ta TUC ke dafifi a harabar ofishin hukumar kula da lantarki ta ƙasar NERC da na kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a faɗin kasar nan domin nuna adawa da ƙarin kuɗin wuta a ƙasar.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin kuɗin wuta ga ƴan rukunin A masu samun wuta tsawon sa’a ashirin a rana.

Lamarin ya fusata al’umma ganin irin halin matsi da ƴan Najeriya ke ciki.

Duk da cewa NERC ta yi nazari kan ƙarin kuɗin amma gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce za su mamaye harabar ofishin hukumar da kuma kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki bayan da wa’adin da suka bayar na ranar Lahadi don hukumar ta soke ƙarin kuɗin ya cika.

Ƙarin kuɗin wutar na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya sakamakon hauhawar farashi da kuma ƙalubalen da ƴan Najeriya suke fuskanta sanadin janye tallafin man fetur.

Sai dai a lokacin da yake kare matakin, ministan lantarki, Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya za ta biya kimanin naira miliyan 1.8 a matsayin kuɗin tallafi na lantarki a kasafin kuɗin 2024.

Ya bayyana cewa dokar lantarki ta 2023 ta ba da izinin a yi nazarin kuɗin wuta sau biyu a shekara.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp