Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC reshen jihar Zamfara, sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, bisa bin umarnin shugabannin kungiyoyin biyu na kasa.
Shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu sun shaidawa manema labarai a Gusau babban birnin jihar cewa sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne domin biyan bukatunsu.
Kungiyar kwadagon ta bayyana cewa yajin aikin ya biyo bayan la’akari da matsalar tattalin arziki da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur da kuma harin da aka kaiwa shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero a jihar Imo kwanan nan.
An samu karancin bin umarnin NLC da TUC na kasa, inda wasu ma’aikata ke ci gaba da gudanar da ayyukansu, wasu kuma sun janye aikinsu a ranar Talata da yamma.
Wannan kafar yada labarai ta ziyarci sakatariyar gwamnatin tarayya ta Yahaya Gusau inda ta lura da cewa wasu tsirarun ma’aikata ne ke shigowa da fita daga cikin sakatariyar.
Shugabannin NLC da TUC na Jihohi, Kwamared Sani Halilu da Kwamared Sa’idu Mudi, bayan sun yi wa manema labarai jawabi, sun koma Sakatariyar Jiha, Jibril Bala Yakubu, da sauran cibiyoyi don tabbatar da bin umarnin saukar kayan aiki.


