fidelitybank

Kungiyar kiristoci ta yi zanga-zanga a kan kisan Filato

Date:

Kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN reshen Filato ta yi wani gangami domin nuna rashin jin daɗinta kan kashe-kashen da ke wakana a jihar da wasu sassan ƙasar.

Gangamin da aka yi wa taken ‘Tattakin zaman lafiya a Filato’ na gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar CAN, Rabaran Polycarp Lubo bisa rakiyar shugaban cocin ECWA, Rabarand Dr Stephen Panya.

Gwamnan jihar ta Filato Caleb Mutfwang ya karɓi baƙuncin masu zanga-zangar a fadarsa da ke Rayfield.

Jihar Filato dai a baya-bayan nan na fuskantar hare-haren ta’addanci inda aka kashe sama da mutum 200 a jajiberin kirsimeti a hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi.

An ƙona gidaje da dama da gonaki a hare-haren da aka shafe dare ana kai wa, an kuma samu mutane da dama da suka jikkata.

Hare-haren da aka kai kan ƙananan hukumomin ya fusata al’ummar Najeriya da ma na ƙasashen duniya inda gwamnan ya caccaki sojoji kan jan ƙafar da suka yi wajen kai ɗauki.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kai ziyara a yankunan bayan hare-haren inda gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin kawo ƙarshen zubar da jinin, sai dai mutane na neman gwamnati ta ɗauki matakan da suka kamata domin kare al’umma a maimakon ɗaukar mataki bayan afkuwar hare-hare.

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp