An zabi Rabaran Daniel Chukwudumebi Okoh, a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ta CAN, Mista Joseph Daramola ya fitar.
Okoh shine Babban Sufeto na Cocin Christ Holy Church, wanda kuma ake kira Nation Builders (Odozi-Obodo).
A halin da ake ciki, PRNigeria ta tattaro cewa, haifaffen Kano kuma dan asalin jihar Ribas, Most Rev. Daniel Okoh, dan Najeriya ne da ya kawar da kabilanci wanda ya kulla abota tsakanin addini da kabilanci, ba a Najeriya kadai ba har ma a fadin duniya. Yana shiryawa da shiga cikin tattaunawa da shirye-shiryen da za su samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya da ci gaba mai dorewa.
Rabaran Okon na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sabani na addini da tashin hankali musamman tsakanin Kirista da Musulmi.
Ana sa ran sabon shugaban kungiyar ta CAN, tare da gogewar da ya samu a tattaunawar tsakanin addinai, zai dauki matakan rage takun saka tsakanin mabiya addinan, musamman tsakanin Kirista da Musulmi a kasar.
An haifi Okoh a ranar 12 ga Nuwamba, 1963 a Kano, iyayen Kirista. Shi dan asalin garin Ndoni ne a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni da ke jihar Ribas a Najeriya.
Ya auri Ngozi kuma sun sami ‘ya’ya hudu. Archbishop Daniel Okoh samfur ne na sanannen makarantar Dennis Memorial Grammar School, Onitsha.
A 1988, ya sauke karatu daga Jami’ar Port-Harcourt a digiri na biyu a fannin Kimiyyar Siyasa da Ilimi.