Kungiyar Kiristoci Ta kasa, CAN reshen jihar Oyo, ta yi kira ga coci-coci da shugabanninsu a jihar da su fara gudanar da addu’o’i da azumi na kwanaki 7.
Wannan roko ya fito ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar CAN na jihar Oyo, Apostle Joshua Akinyemiju ya fitar ranar Juma’a a Ibadan.
Ya ce, za a fara gudanar da addu’o’i da azumi ne daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Yuli.
Akinyemiju ya ce, rana ta bakwai za ta zama godiya ga amsa addu’o’in da aka yi.
“Babban addu’o’inmu na tsawon kwanaki bakwai ya kamata su shafi maido da zaman lafiya da tsaro a Oyo da Najeriya baki daya.
“Wannan yana da matukar muhimmanci da gaggawa; Allah ya tashi ya halakar da duk makiya da ke adawa da zaman lafiya a Najeriya cikin sunan Yesu,” inji shi.