Kungiyar kiristocin ta kasa a ranar Larabar nan ta bukaci shugabannin masu fafutukar kafa kasar Biafra da su dakatar da aikata laifuka da kashe-kashe, bisa zargin fafutukar neman yancin kai.
Wannan dai shi ne kamar yadda kungiyar kolin kiristoci ta kuma yi Allah wadai, da kakkausar murya, kisan gillar da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi wa Lady Fatima da ‘ya’yanta hudu da ba su ji ba ba su gani ba.
A cewar Punch, kungiyar kiristocin ta yi wannan bukata ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Fasto Adebayo Oladeji, mataimaki na musamman ga shugaban CAN, Rev Dr Samson Ayokunle.
Kungiyar ta CAN ta kuma bukaci a yi adalci ga wadanda abin ya shafa tare da yin kira ga jami’an tsaro da su kamo wadanda ke da hannu a wannan aika-aika domin kawo karshen kashe-kashen rashin hankali a kasar.