Ƙungiyar cigaban al’ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta zaɓi Sanata John Azuta-Mbata a matsayin sabon shugabanta.
An zaɓi Sanata Azuta-Mbata, tsohon ɗan majalisar dattawa daga jihar Rivers a lokacin taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar da ya gudana a birnin Enugu ranar Juma’a.
Gwamnonin jihohin yankin kudu maso gabashin ƙasar biyar da shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki daga ƙabilar Igbo ne suka halarci taron zaɓen sabon shugaban.
Sanata Azuta-Mbata shi ne shugaban ƙungiyar na 13, bayan da ya gaji Fidelis Chukwu ɗan jihar Imo da ya kammala wa’adin mulkinsa.
Sabon shugaban ya alƙawarta tafiya da kowa wajen gudanar da shugabancinsa, domin haɗa kan ‘ya’yan ƙungiyar da kuma ci gaban al’ummar ƙabilar Igbo.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu maso gabashin Najeriay, Hope Uzodinma ya tabbatar wa ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo cewa gwamnonin yankin za su bai wa shugabancin ƙungiyar goyon baya da haɗin kai, domin ciyar da yankin gaba.
Tuni dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga sabon shugaban ƙungiyar ta Ohanaeze Ndigbo.