fidelitybank

Kungiyar Gwamnoni sun taya Ganduje murnar cika shekaru 73

Date:

Kungiyar Gwamnonin Progressive Governors Forum (PGF), ta bi sahun ‘yan Najeriya wajen taya Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 73 da haihuwa.

A cikin wata sanarwa da shugaban PGF, Abubakar Atiku Bagudu ya fitar, ya yabawa jagorancin Ganduje da jajircewarsa wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba.

Ya ce, “Gwamnan Progressive Governors Forum (PGF) na tare da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano domin bikin cikarsa shekaru 73 a duniya. Tare da al’ummar jihar Kano, da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa, muna taya ku da iyalanku murnar wannan rana ta musamman.

“Muna yaba wa jagoranci, hangen nesa da kuma jajircewar ku wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba a dunkule, karkashin jagorancin jam’iyyar mu ta APC. Muna godiya da irin gudunmawar da kuke baiwa tawagar Gwamnonin Cigabanmu ta hanyar basirar ku da kuma jajircewar ku akan hanyoyin tafiyar da harkokin mulki a jihar Kano da ma a matakin kasa baki daya. A matsayinka na Gwamnan Jihar Kano, ta hanyar duk wasu tsare-tsare na ci gaba da gwamnatinka karkashin jam’iyyar APC ke aiwatarwa, muna tabbatar da cewa kai shugaba ne na gaskiya mai son ci gaba da kirkire-kirkire.

“A yayin da muke murna da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, muna kuma kara jaddada aniyarmu ta hadin gwiwa wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su karfafa karfin jihohinmu masu ci gaba wajen samar da ayyukan yi, rage rashin daidaito da kuma rage radadin talauci a Najeriya.

“Sai kuma ina taya Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murnar zagayowar ranar haihuwarsa.”

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...
X whatsapp