Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 a birnin Landan.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wanda shugabanta, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya fitar, ya ce Buhari tamkar uba yake a gare su.
“Muna miƙa ta’aziyarmu ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da iyalai da ƴanuwa da mutanen jihar Katsina da ma ƴan Najeriya baki ɗaya bisa wannan babban rashin da aka yi.”
Gwamnonin sun ce Buhari abin alfaharin yankinsu ne, “wanda ya ƙarar da rasyuwarsa wajen hidima da sadaukar da kansa wajen ciyar da Najeriya gaba.”
“Saboda wannan ne ƙungiyar gwmnonin arewa maso yamma suka amince da ayyana ranar Talata, 5 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar hutu domin jimamin rasuwar mamacin,” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Dikko Radda ya ce gawar Buhari za ta isa Katsina a gobe Talata da misalin ƙarfe 12, sannan a gudanar da jana’izar da misalin ƙarfe biyu na rana.
“Muna kira ga dukkan ƴan Najeriya su yi masa addu’a. Allah ya jiƙansa, sannan muna addu’ar Allah ya ba iyalana da ma dukkan ƴan ƙasar juriyar rashinsa.”