fidelitybank

Kungiyar gwamnoni da Buhari sun gana da Emefiele

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi ganawar sirri da shugaban ƙungiyar gwamnoni ta kasa, Aminu Waziri Tambuwal, da shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC Atiku Bagudu kan matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi da ƙasar ke fuskanta.

Daga cikin waɗanda suka halarci zaman har da gwamnan Babban Bankin ƙasar Godwin Emefiele da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar Abdulrasheed Bawa da kuma babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar Janar Lucky Irabor.

An yi ganawar ne a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja.

Karanta Wannan: An jibge jami’an tsaro a ofishin CBN

Da farko an tsara zaman da ƙungiyar gwamnonin ƙasar, to sai dai daga baya an soke zama da duka gwamnonin sakamakon wasu dalilai da ba a bayyana ba.

Bayyanar gwamnan Babban Bankin a ganawar alama ce da ke nuna cewa an tsara zaman ne domin tattauna batun matsalar ƙarancin kuɗi, da ke fuskantar suka daga ‘yan ƙasar, ciki har da gwamnonin ƙasar.

A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasar ya gana da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, inda wasu daga cikin gwamnonin suka yi kira ga shugaban ƙasar da ya shiga tsakani domin bayar da dama a ci gaba da amfani da tsoffi da abbin takardun kuɗin a faɗin kasar.

To sai dai rahotonni sun ce shugaban ƙasar ya yi watsi da buƙatar kasancewar kotu ta haramta wa gamnati sake ƙara wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Wasu majiyoyin a fadar shugaban ƙasar sun tabbatar da cewa shugaban ƙasar na kaffa-kaffa, kada ayi masa kallon mai watsi da dokoki.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp