Wani kumbo da Indiya ta tura yayi nasarar sauka duniyar wata, abin da ya sa Indiyar ta zama ƙasa ta hudu a duniya da ta yi nasarar yin hakan.
A lokacin da yake shirin sauka kumbon mai suna Chandrayan 3 ya sassauta saurinsa har sai da ya kai saura mita ɗari daya tsakaninsa da doron watan sannan ya sauka cikin nasara.
Dukkanin wannan an yi shi ne ta hanyar sarrafa kumbon daga nesa.
Indiya ta samu nasarar yin hakan ne yan kwanaki bayan da Rasha ta yi yunkurin yin hakan amma ba tare da yin nasara ba.
Firaiministan Indiya Narendra Modi ya ce gagarumin aikin ƙasar ya bayar da fifiko ga amfani da fasahar ɗan’adam don haka nasarar ta ƴan ƙasar ne da ƙasar.
Daga bisani kumbon zai tura wata na’ura da za ta lalubo inda ake da ƙanƙara abin da zai ba shi damar kafa mazauni na dindindin bisa doron wata.


