fidelitybank

Kujerar shugaban marasa rinjaye ta haifar da cacar baka a majalisa

Date:

An samu takaddama a majalisar dattijai, bayan sanar da nadin shugabanni a bangaren marasa rinjaye da Shugaba Majalisar Godswill Akpabio ya yi.

Kujerar shugaban marasa rinjaye da ta mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye sun kasance babu kowa tun bayan da kotun daukaka kara ta soke zaben Sanata Simon Davou Mwadkwon na PDP da Darlington Nwokocha na LP.

Kotu ta soke zaben sanata Simon Mwadkwon inda ta ba da umarnin sake gudanar da zabe.

Tun a makon jiya ne sanatocin jam’iyyar PDP suka gudanar da wani taron gaggawa kan batun maye guraben shugabannin marasa rinjaye.

Jaridar Punch ta ambato Sanata Garba Maidoki wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron, na cewa ‘yan majalisa bangaren adawa sun amince da fitar da sabon shugaban marasa rinjaye daga arewa ta tsakiya.

Don haka, yayin zaman majalisar na Talata, Godswill Akpabio ya sanar da Abba Moro na PDP a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Osita Ngwu shi ma daga PDP zai kasance mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye.

Shugaban majalisar ya ce sabbin shugabannin marasa rinjayen sun samu rinjayen goyon bayan takwarorinsu.

Da yake gabatar da wanai kudurin jan hankali, Sanata Okechukwu Ezea na jam’iyyar LP ya nuna rashin amincewa da rashin shigar da jam’iyyarsa a shugabancin marasa rinjaye, inda ya bayyana lamarin a matsayin rashin adalci ga jam’iyyun marasa rinjaye.

Ana cikin hargitsi ne, sai Sanata Tony Nwoyi na LP ya zargi Godswill Akpabio da nada wa jam’iyyun adawa shugabanci.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp