Ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ya bukaci a saki sauran mutane da ake rike da su cikin akuba sakamakon zanga-zangar Endsars.
Kirayen Amnesty na zuwa ne bayan sakin mutum 9 daga cikin gwamman masu zanga-zangar da ake garkame da su a fursunoni daban-daban na Najeriya.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Amnesty ta ce binciken ta na watan Oktoban 2022 ya nuna cewa ana rike da sama da masu zanga-zanga 40.
Sanarwar ta kuma kara da cewa abin takaici shi ne ganin har yanzu anki yarda ‘yan uwa da lauyoyin masu zanga-zangar su gana.
Zanga-zangar ta EndSARS wadda aka fara a Legas da Abuja a watan Oktoban 2020, ta kuma fantsama zuwa wasu jihohin kasar, kafin daga bisani ta rikiÉ—e ta koma rikici, abun da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.
Masu zanga-zangar sun zargi jami’an tsaro da buÉ—e masu wuta a Lekki da ke jihar Legas, wato cibiyar inda ake gudanar da zanga-zanar, abin da ya janyo jikkatar mutane da dama.
Zanga-zangar ta ja hankalin duniya sosai inda har shahararrun mutane a fadin duniya suka dinga tsoma baki suna nuna goyon baya ga masu yin ta.