fidelitybank

Kudirin dokar zabe: Rashin wayewa ne ya s wasu ke ganin Buhari na jan kafa

Date:

Fadar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce, jahilci ne ya sa wasu ke ganin Shugaban Ƙasa ke jan-ƙafa wajen saka wa sabon ƙudirin dokar zaɓe hannu, wanda Majalisar Tarayya ta miƙa masa tun a watan Janairu.

A kwanan nan ne wasu ƙungiyoyin farar hula suka dinga sukar shugaban saboda bai saka wa sabon ƙudirin dokar hannu ba a karo na biyu bayan Majalisar Tarayyar ta yi mata kwaskwarima tare da sake aika wa Buhari.

Wata sanarwa da fadar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, shugaban ƙasa na da kwana 30 domin yin nazari kan ƙudirin, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya ba shi dama.

“Sai dai a tausaya musu saboda jahiltar Kundin Tsarin Mulki da suka yi saboda shugaban ƙasa na da kwana 30 da zai iya saka mata hannu ko kuma akasin hakan bayan Majalisa ta miƙa masa dokar,” in ji sanarwar.

“A bayyane take cewa an miƙa wa shugaban ƙasa ƙudirin ranar 31 ga watan Janairun 2022, abin da ke nufin gwamnati za ta iya nazari cikin tsanaki har zuwa 1 ga watan Maris kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.”

Tun farko Buhari ya ƙi amincewa da sabuwar dokar yana mai cewa ‘yan majalisar ba su ba wa jam’iyyu zaɓi ba wajen maganar zaɓen fitar da ‘yan takara, inda suka ce zaɓen ‘yar tinƙe kaɗai za a bi. Daga baya sun gyara sannan suka sake miƙa wa shugaban. In ji BBC.

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp