fidelitybank

Kudin da NNPC ke kashewa a tallafin mai ya wuce tunani – Hamid Ali

Date:

Shugaban Hukumar fasa Kauri ta Najeria wato Kwastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya ce, Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPC, ba zai iya kare matakin yawan makudan kudaden da yake kashewa na tallafin mai a kowacce rana ba, inda hakan ya janyo ana ɓatar na sama da naira biliyan shida a duk shekara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Hamidu Ali ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis, a gaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke sauraren bayani kan tsarin kashe kudi daga shekarar 2023 zuwa 2025 na matsakaicin zango.

Ya kara da cewa babu yadda NNPC zai yi bayanin ikirarin ana amfani da lita miliyan 98 a kowacce rana, inda ya yi zargin kamfanin na kara lita miliyan 38 kan ainahin wanda ake amfani da shi a kowacce ranar.

Kwamitin ya buƙaci shugaban hukumar kwastam din da ya yi bayani kan gibin da aka samu na tsakanin naira tiriliyan 11 zuwa 12 na kasafin badi.

Gwamnatin Najeriyar dai ta shigar da bukatar kasafin kudin shekara mai zuwa da ya kai naira biliyan 19.76, kuma za a samu gibin tsakanin sama da biliyan 11 zuwa sama da biliyan 12.

assu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp