Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce, Najeriya ce ta fi dacewa masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Washington DC yayin da yake wata tattaunawa ta musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya da kuma zauren masu zuba hannun jari, a wani taro da kungiyar hadinkan Amurka da Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, a gefen taron shugabannin Afrika da Amurka.
Cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ya fitar, ya ce “yana da matukar kyau in maimaita wannan, cewa Najeriya na da faffadan tattalin arziki.
Kuma na farko tana da yawan al’umma ita ce tafi kowacce kasar Afrika karfin tattalin arziki, babu shakka kuma Najeriya ce kan gaba wajen sayen kayayyaki da ake kai wa nahiyar.”