fidelitybank

Ku zabi Peter Obi a ranar Asabar – Pa Ayo Adebanjo

Date:

Pa Ayo Adebanj,o ya roki ‘yan Najeriya da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi, ranar Asabar.

Shugaban kungiyar Yarbawa koli, Afenifere ya zayyana kuri’u ga Obi a wata ganawa da kungiyar Atunluse Initiatives.

Dattijon ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar al’adu da siyasa ta Yarbawa a ranar Talata a Legas, kamar yadda NAN ta ruwaito.

Karanta Wannan: Zan magance rashin aikin yi ga matasa – Obi

Adebanjo ya ce jama’a na bukatar tsohon gwamnan Anambra don ceto Najeriya daga kangin talauci da rashin shugabanci.

“Duk ‘yan kasa suna da alhakin gwagwarmayar kwato ‘yancinsu ta hanyar zaben shugaban kasa na karshen mako,” in ji shi.

“Ba mu da kudi don yakar su, amma dole ne mu yi duk abin da ya dace don ‘yantar da kanmu,” in ji shi.

Adebanjo ya ci gaba da cewa, akwai yarjejeniyar da aka kulla cewa za a raba madafun iko a cibiyar tsakanin Arewa da Kudu.

Basaraken ya tuna cewa Kudu-maso-Yamma sun yi zamaninsu a karkashin Olusegun Obasanjo da kuma Arewa a karkashin Umaru Yar’Adua.

“Goodluck Jonathan ya yi nasa daga Kudu-maso-Kudu, ya koma Arewa. Yanzu idan muka dawo Kudu, a ba yankin Kudu-maso-Gabas da sunan adalci,” inji shi.

Shugaban kungiyar Atunluse, Akinsola Akinbobola da tawagarsa daga baya sun yi ganawar sirri da Adebanjo da sauran shugabannin kungiyar ta Afenifere.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp