Dada Olusegun, mai baiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a kan kafafen yada labarai na zamani, ya musanta ikirarin da ake yi na karawa gwamnoni da alkalai da mataimakan siyasa kashi 114 cikin 100 na albashi.
Olusegun ya bayyana hakan ne a daren Laraba ta shafin sa na Twitter.
Martanin mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yada labarai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin karin albashi na kashi 114 na shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, alkalai da mataimakan siyasa.
“Ku yi watsi da karyar da wasu kafafen yada labarai ke yi na cewa gwamnati ta amince da karin albashin mataimakan siyasa kashi 114 cikin 100. Labaran karya ba za su iya ba kuma ba za su taba yin nasara ba,” ya rubuta.
Da yake tabbatar da matsayin Olusegun, Jami’in Hulda da Jama’a na RMAFC, Christian Nwachukwu, ya shaida wa Jaridar Leadership cewa Tinubu bai amince da karin albashi ga wadanda aka fallasa a siyasance ba.
A halin da ake ciki, a baya, kwamishiniyar tarayya a hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba, ta yi tsokaci kan karin albashin lokacin da ta wakilci shugaban RMAFC, Mohammad Shehu a wajen gabatar da rahoton kasafin kudin da aka duba ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a Birnin Birnin Kebbi, ranar Talata.


