Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP a 2023 babban zaben kasar, yana mai cewa an gaza.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a jiya a wata ziyara da ya kai wa Sarkin Jama’a a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a a Kudancin Jihar Kaduna.
Ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai farfado da fannin ilimi tare da tabbatar da cewa yaran da ba sa zuwa makaranta da marasa galihu sun samu hanyar komawa makaranta.
Ya ce, “Na yi shi a jihar Kano kuma a matakin tarayya zan yi. Zan gina azuzuwa 500,000 ga yaran da ba su zuwa makaranta don tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar yin karatun firamare kyauta da tilas.”
‘Kaddamar da kudin makaranta zai kashe ilimi a Arewa’
‘Yan sanda sun kama wasu mutane 5 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
Ya kuma yi alkawarin biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai, tare da bayar da tallafin karatu ta atomatik ga daliban da suka fi kwarewa a fannoni daban-daban don yin karatu a ko ina a duniya.