Shugaba Muhammadu Buhari, ya nemi ‘yan takarar a zaben 2023 su guji keta rigar mutunci da tunzura jama’a a yakin neman zabensu.
Shugaban ya yi gargadin cewa karuwar labaran jabu da karkatattun labarai na ci gaba da zama gagarumar barazana ga tsarin dimokradiyyar Najeriya.
Ya ce labaran jabu na dauke hankali daga yin yakin neman zabe bisa manufa maimakon haka sai a yi ta kwarzanta yiwuwar cin mutuncin mutane da zaga-zage da harzuka mutane.
Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabi ne a wani sakon bidiyo da ya gabatar a taron sa hannun ‘yan takarar shugaban kasa don tabbatar da zaman lafiya a zaben 2023.