Babban kamfanin rarraba wutar lantarki na Malawi, ya fitar da wata sanarwar ban hakuri bayan daukewar wutar lantarki a daukacin kasar.
Kamfanin ya ce ya na aiki tukuru domin ganin an samu wutar lantarkin, bayan daukewarta baki daya a yammacin jiya Asabar.
Al’ummar Malawi na daga cikin matalauta a duniya, Bankin Duniya ya ce kashi 15 cikin su ne ke samun wutar lantarki.
Ga wadanda suke samun lantarkin kuwa, kullum cikin zullumi suke na daukewarta a kowanne lokaci.
A watannin da suka gabata dai Malawi na fama da ƙarancin wutar lantarki, ko a watan Janairun shekarar nan, an shafe kwanaki uku babu wuta a kasar bayan guguwar Ana da ta afkawa kudancin Africa. A cewar BBC.